Syria ta ba da umarnin gudanar da bincike akan kisan Hariri
October 30, 2005Talla
Shugaban Syria Bashar al-Assad ya ba da umarnin gudanar da bincike akan kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. Kwamitin binciken dai zai yiwa fararen hula da jami´an sojin Syria tambayoyi sannan kuma zai ba da hadin kai ga jami´an MDD masu binciken wannan kisa. A cikin rahoton da ya gabatarwa kwamitin sulhu na MDD a kwanakin baya, mai daukaka kara na Jamus Detlev Mehlis wanda ke jagorantar binciken ya zargi manyan jami´an leken asirin Syria da na Lebanon da hannu a kisan na Hariri. Mehlis ya kuma zargi gwamnatin Damascus da rashin ba da hadin kai a binciken da yake yi. Hariri da wasu mutane 20 sun mutu a wani harin bam da aka kai a birnin Beirut a cikin watan fabrairu da ya gabata.