Taƙadama tsakanin Libiya da Ingila
August 20, 2010Talla
Gwamnatin ƙasar Britaniya ta yi kashedi ga ƙasar Libiya wajan gudanar da bukukuwan zagayowar cikar shekara guda da sakin Abdelbaset Al-Megrahi.
Mutuman da ke da alhakin kai hari Lokerbie a shekara ta 2001 wanda a cikinsa mutane 270 suka rasa rayukansu.
Wani mai magana da yawun gwamnatin ya bayyana cewa duk wani shagali da hukumomin ƙasar ta Libiya zasu shirya zai zama tamkar zagi ga ƙasar.
An dai saki Al-Megrahi ne a cikin watan Augusta na shekara bara daga wani gidan bursunan da ake tsare da shi a ƙasar Ekosiya, kan hujar cewa ba zai yi watanni ukku ba a raye
Tun da farko dai friministan Britaniyan David Cameron ya shaida cewa sakin na al-Megrahi wani babban kuskure ne
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar