1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama kan kisan mutane 93 a Siriya

May 27, 2012

Mahukuntan Siriya sun musanta zargin da 'yan adawa suka yi musu na hallaka mutane casa'in da uku (93) a garin Haula wanda aka yi ranar Juma'a.

Syrien Massaker in HuolaHoto: Reuters

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen ƙasar ta Siriya Jihad Makdissi ya ce ko kusa mahunkuntan ƙasar ba su da hannu a wannan kisan gillar da aka yi.

Mr Makdissi ya ƙara da cewa wasu ɗaruruwan 'yan bindiga ne ɗauke da manya makamai su ka aikata kisan domin a cewarsa baya ga mutanen da aka kashe, 'yan bindigar sun hallaka wasu dakarun gwamnatin ƙasar guda uku a yankin.

Masu rajin kare haƙƙin bani adama a yankin na Haula dai sun yi watsi da wannan kalaman na gwamatin inda su ka ce sojin gwamnati ne ke da hannu a kisan domin a cewarsu dakarun gwamnati sun yi luguden wuta kan masu zanga-zanga na tsawon lokaci bayan kammala sallar Juma'a.

Tuni dai mahukuntan na Siriya su ka kafa wani kwamiti da zai gano wanda ke da hannu kan wannan batu wanda ya sanadiyyar rasuwar ƙananan yara talatin da uku da kuma manya sittin.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh