Taƙaddama tsakanin China da Japan
December 13, 2012![©Kyodo/MAXPPP - 02/09/2012 ; NAHA, Japan - Photo taken from a Kyodo News helicopter shows Uotsuri Island, part of the Senkaku Islands in the East China Sea on Sept. 2, 2012. A Tokyo metropolitan government team the same day conducted an offshore inspection of the islands as part of its plan to buy land on the isles amid a growing territorial row with China over the uninhabited islets. (Kyodo)](https://static.dw.com/image/16250347_800.webp)
Rikici tsakanin ƙasar China da Japan a kan tsibirin Senkaku, ya ƙara zafafa,bayan da Japan ta sanar da cewar wani jirgin sama bincikke na yaƙi na ƙasar ta China ya keta sararin samaniyarta a karon farkon tun da ricikin ya rincaɓe a cikin watan Satumbar da ya gabata,a lokacin da wani ɓangaran tsibirin ya zama mallakar Japan.
Kakkakin gamnatin ta Japon Osamu Fujimura ya ce sun aike da jiragen yaƙi guda fudu a sansani ,sai dai ya ce babu wata karawa da aka yi tsakanin jiragen na ƙasashen biyu.China ta buƙaci Japan da ta dai'na, gudanar da harkokin a cikin ruwayen da sararin samaniyar tsbirin na Diayou wanda ta ce mallakarta ne.Wannan al'amari ya faru ne a sa'ilin da ƙasar China ke gudanar da bukukuwan nuna juyayi na zagayowar cikkar shekaru 75 da aikata kisan kiasun da Japan ta yi a kan yan China a garin Nankin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abass