Taƙaddama tsakanin Japan da China
October 16, 2012Bisa ga dukkan alamu rikicin kasashen China da Japan ya fara ɗaukar wani sabon salo, Inda yanzu kasashen biyu suka dauki matakin shiga cikin shirin ko-ta-kwana, a yayinda dakarun kasashen biyu ke cikin shirye-shiryen kasancewa a bakin daga. Wanna rikicin ya ɗauko asalinsa ne bisa wasu tsibirai da kasashen biyu ke taƙaddama akansu. Kasar China ta jibge a kalla wasu manyan jiragen yakin ruwanta takwas, a kusa ga kasar Japan yayinda kasar ta Japan ta ce tuni dakarun kasasrta ke cikin shirin ko-ta-kwana, domin maida martani ga duk wani yunkurin kasar China, na aukawa Japan. Saktarin janar na MMD Ban Ki-moon ya kira kasashen biyu da su kai zuciya nesa, domin kaucewa duk wani tashin hankali a dai-dai lokacin da duniyar ke cikin wasu riginginmu.
Mawallafi: Usman Shehu Usma
Edita: Umaru Aliyu