1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama tsakanin Pakistan da NATO na ƙara yin tsami

November 29, 2011

Pakistan ta ce in dai batun ƙoƙarin warware rikicin Afghanistan ne, to, kuwa babu hannun ta a ciki

Shugaban Pakistan Asif Ali ZardariHoto: AP

Pakistan ta sanar da ƙaurace wa taron da za'a gudanar a birnin Bonn da ke tarayyar Jamus dangane da Makomar Afghanistan a mako mai zuwa. Wani jami'in gwamnatin Pakistan ne ya shaidar da hakan bayan ganawar majalisar zartarwar ƙasar a birnin Islamanad. Hakan dai na a matsayin martanin Pakistan dangane da harin sojojin ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO akan iyakokin Pakistan da Afganistan, daya kashe sojojinta 24.

Kafin cimma wannan matsayi a ɓangaren mahukunta a birnin Islamabad dai, mahukunta a birnin Washington sun yi kira ga Pakistan data halarci taron nemo hanyar warware matsalar Afganistan da zai gudana ranar 5 ga watan Disamba. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka a birnin Washington ya bayyana muhimmancin samun kyakkyawar danganta a tsakanin Amurka da Pakistan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita Zainab Mohammed Abubakar