1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar gwamnatin Afghanistan da NATO

Matthew ZuvelaMarch 7, 2011

Wata taƙaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatin Afghanistan da Ƙungiyar ƙawance ta NATO dangane da kisar farar hular da ya afku bisa kuskure

Shugaba Hamid KarzaiHoto: AP / Fotomontage: DW

Sakataren tsaron Amurka, Robert Gates, ya isa Afghanistan, inda ya kai wata ziyarar bazata zuwa ga dakarun sojojin Amurkan da ke ƙasar. Wannan dai ya zo a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Afghanistan da ƙungiyar ƙawance ta NATO ke tsami, bayan da wani jirgi mai saukar ungulu ya yi sanadiyyar hallakar wasu ƙananan yara tara bisa kuskure, a lokacin da ta kai wani hari.

Duk da cewa kwammandan ƙungiyar ƙawance na NATOn David Patreus, ya bada haƙuri kuma ya yi ta'aziyya ga gwamnatin ta Afghanistan, shugaba Hamid Karzai ya ce ba zasu lamunta da cewa kisan ya afku ne bisa kuskure ba.

Ƙasar Jamus na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da dakaru a ƙungiyar ƙawancen ta NATO da ke Afgahnistan, inda ta ke kimanin dakaru 4,500

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Abdullahi Tanko Bala