1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar Isra'ila da Falasɗinu

March 13, 2011

Falasɗinawa sun yi Allah Wadai da shirin Isra'ila na ƙara matsugunan Yahudawa a yankunan su

Shugaba Obama da Firaministan Isra'ila Netanyahu, da kuma shugaba Abbas na FalasɗinuHoto: AP

Hukumar Falasɗinu ta yi kakkausar suka ga amincewar da hukumomin Isra'ila suka yi na gina ɗaruruwan sabbin gidaje a yankunan Yahudawa 'yan-kama wuri zauna dake Gaɓar Tekun Jodan. Babban mai shiga tsakani na ɓangaren Falasɗinawa a tattaunawar samar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya Saeb Erakat ya ce akwai buƙatar rukunin masu shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa daya ƙunshi Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai da kuma Amirka su sanya baki domin hana Isra'ila ci gaba da aiwatar da wannan matakin.

A yau Lahadi ne gwamnatin Isra'ila ta ce majalisar ministocin ƙasar ta amince da samar da ɗaruruwan sabbin gidaje a huɗu daga cikin yankunan da Yahudawa 'yan-kama wuri zauna suke a Gaɓar Tekun Jordan. Yanke shawarar dai ta zone ƙasa-da-Sa'oi 24 bayan da aka daɓawa wasu matasa biyu da ƙananan yara uku wuƙa - har lahiya yayin da suke kwance akan gadajen su a yankin Itamar dake kusa da Nablus, abinda yasa 'yan-kama wuri zaunan suka cinna wuta akan wani gidan Ba -Falasɗine dake kusa da yankin. Majalisar Ɗinkin Duniya dai tace manufar Isra'ila ta faɗaɗa gine-ginen ne babban tarnaƙi ga sake komawa bisa teburin shawarar samar da zaman lafiya a yankin na Gabas Ta Tsakiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala