1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar siyasa a Tanzaniya.

February 28, 2011

Gwamnatin Tanzaniya ta zargi 'yan adawa da ƙokarin haddasa tashin hankali a tsakanin al'ummar ƙasar

Shugaba Jakaya Kikwete yayin wata hira da Deutsche WelleHoto: DW

A ranar Litinin 28 ga watan Fabrairun 2011 ne shugaba Jakaya Kikwete na ƙasar Tanzaniya ya zargi babbar jam'iyyar adawar ƙasar da ƙoƙarin haddasa fitina da nufin kawar da gwamnatinsa. Shugaban ya yi wannan zargin ne bayan da dubbannin masu zanga-zanga suka yi jerin gwano a ranar 24 ga watan Fabrairu yayin da jam'iyyar Chadema Party ta shirya wata zanga-zangar lumana a Mwanza, birni na biyu mafi girma a ƙasar. Bayan zanga-zangar ce kuma shugabannin adawar suka ɗeba wa gwamnati wa'adin kwanaki tara ta daidaita tattalin arziƙin ƙasar, kana ta shawo kan matsalar cin hanci da rashawa da kuma samar da sabon tsarin mulki, ko kuma ta fuskanci gagarumin bore - makamancin na ƙasashen Masar da Tunisia. Shugaba Kikwete, wanda aka sake zaɓan sa a ranar 31 ga watan Oktoba a zaɓukan da aka yi zargin tafka maguɗi da ƙarancin masu jefa ƙuri'a, ya zargi jam'iyyar Chadema da ƙoƙarin ingiza zubar da jini a ƙasar. Sai dai kuma 'yan adawar suka ce a wannan Talatar ce za su mayar da martani ga zargin da shugaban ya yi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita: Halima Balaraba Abbas