Taɓa Ka Lashe: 20.01.2010
January 22, 2010Talla
A kowace shekara al´umar garin Kagoro dake a jihar Kaduna ta tarayyar Najeriya na gudanar bikin al´adun gargajiya na Afan Festival, wanda a ciki suke baje kolin ɗinbim kayakin al´adunsu na gargajiya. Al´umar wannan gari na amfani da wannan bikin domin kyautata hulɗa tsakaninsu da sauran ƙabilun Najeriya.