1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓarɓarewar aikin agaji a Libiya

May 19, 2011

MƊD ta koka game da rashin samun damar kaiwa jama'a agaji a Libiya

Tambarin hukumar agaji ta MƊD (UNHCR)Hoto: DW-Montage

Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi gargaɗin cewar yanayin matsalar masu neman agaji a ƙasar Libiya yana ƙara taɓarɓarewa, bayan duk wani yunƙurin da aka yi domin neman tsagaita buɗe wuta da nufin kai agaji ga yankunan 'yan tawayen da aka yiwa ƙawanya ya ci tura. Jami'an

Majalisar Ɗinkin Duniya suna ta gudanar da taruka tare da shugaba Muammar Gadhafi na ƙasar Libiya, da 'yan tawayen ƙasar da kuma ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO domin samun tabbacin tsaron da zai ba ma'aikatan bayar da agajin majalisar damar isar da abinci da magunguna da kuma ruwan sha zuwa ga mabuƙata.

A halin da ake ciki kuma tashoshin telebijin na Larabci sun ambaci ma'aikatar kula da harkokin cikin gida a ƙasar Tunisia na ƙaryata labarin cewar Uwargidar Gadhafi da kuma 'yarsa sun shiga ƙasar a kwanakin baya. Dukkan matan biyu suna cikin jerin sunayen waɗanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanyawa takunkumi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu