1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mayakan waje na dafa wa Boko Haram

January 17, 2025

Rundunar sojojin Najeriya ta ce taimakon da bangarorin kungiyoyin Boko Haram suke samu ta hanyar shigowar mayaka daga kasashen waje, shi ne ya haifar da farfadowar hare-hare da suke kai wa a jihar Borno.

Najeriya | Sojoji | 'Yan Ta'adda | Boko Haram
Sojojin NAjeriya dai, sun jima suna yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a kasarHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Masana tsaro da al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar dai, na nuna damuwa kan yadda jami'an tsaron suka kasa hana irin wadannan mayaka shigowa kasar. Bangarorin mayakan Boko Haram sun zafafa hare-haren da suke kai wa kan jami'an tsaro da fararen hula a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya, bayan kwashe lokacin ana morar zaman lafiya a yankuna da dama na jihar Borno da ma sauran sassan Arewa maso Gabas din.

Karin Bayani: Hare-haren kunar baklin wake sun salwantar da rayuka a Najeriya

Yayin da ake ganin kasawar jami'an tsaro wajen magance hare-haren ne, rundunar sojojin Najeriyar ta ce mayakan na Boko Haram da sauran 'yan ta'adda na samun taimako daga 'yan uwansu wadanda suke shigowa daga kasashen waje. A cewar mai mamana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba hare-hare da mayakan Boko Haram suka kai a Kareto da Wajiroko da Chibok da Gwoza da Sabon gari da Dumba duk a jihar Borno, na da alaka da shigowar mayakan daga ketare.

Ci gaba da karatu a jami'ar Maiduguri duk da kalubalai na tsaro

03:27

This browser does not support the video element.

#b#Wannan ya haifar da rudani da tashin hankali tsakanin al'ummar jihar Borno, ganin bayan samun zaman lafiya yanzu hare-hare na dawo wa. Sai dai masana da masharhanta da ma talakawan wannan yankin, na yin mamaki yadda wadannan mayakan za su shigo ba tare da jami'an tsaro da ake da su a kan iyakoki sun hana su ba. Farfesa Lawal Jafar Tahir na jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu ya ce ba sabon abu ba ne shigowar mayakan, amma dai a wannan lokaci yana da alaka da tsamin dangata tsakanin Najeriya da makwabtanta.

Karin Bayani: Tsaro na tabarbarewa a Arewa maso gabashin Najeriya

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa ya bayyana cewa yana zargin ana taimaka wa 'yan ta'addan na Boko Haram da kudi da manyan makamai ta hanyar wasu kungiyoyin masu zaman kansu daga kasashen ketare, duk kuwa da cewa bai ambaci wani ko  wata kasa ko ma kungiya da yake zargi ta ba su tallafin ba.