Ta'addancin na kara yaduwa a yankin Sahel
March 25, 2022Za mu fara da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta mai taken "Idan sannu a hankali ta'addanci ya fara matsowa kusa". Jaridar ta ce a jamhuriyar Benin, mutane na zaman lafiya da juna, sai dai sannu a hankali ayyukan ta'addanci na yaduwa daga jamhuriyar Nijar da Burkina Faso. Hakan ya haifar da rashin yarda da juna tsakanin al'uma. A yankin arewacin Benin dai ana ci gaba da fiuskantar hare- haren 'yan ta'adda, inda a karshen watan Nuwanban shekarar da ta gabata kadai cikin wata guda an kai hare-hare sau uku a garuruwan Porga da Banikoara. Kana a cikin watan Fabrairun da ya gabata a katafaren wurin shakatawa sama da mutane 10 ne suka rasa rayukansu a harin.
Ayyukan ta'addanci na bazuwa daga Nijar Burkina Har zuwa Jamhuriyar Benin
Ana fassara halin da ake ciki a Benin da mahara daga wadannan kasashe biyu ne ke shiga Benin, ma'ana hari ne daga baki na ketare amma ba cikin gida ba. A cewar Mohamed Tourare da ke zama limamin babban masallacin garin Parakou dai, suna zaman lafiya kuma rayuwa na tafiya kamar yadda aka saba, kasancewar garin baya kan iyakar kasar, duk da cewar ba su da nisa da iyakar sosai. Akasarin mazauna Parakou dai Musulmi ne, kuma suna rayuwa da Kiristocin garin lami lafiya ba tare da wata matsala ba. Kuma bangarorin biyu na kokarin ganin cewar sun yarda da juna duk da barazanar wadannan rikice-rikice.
Karancin Abinci a duniya da yunkurin kara daidaihulda da sauran ksahen saboda yaki tsakanin Rasha da UkraineHukumar gudanarwar tarayyar Turai na son tallafa wa mana, domin samar da abinci a Afrika" da haka ne jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bude sharhin da ta rubuta game da halin da duniya ta tsinci kanta a ciki. Harin da Rasha ta afkawa Ukraine da shi ya haifar da fargaba a Turai ba wai don yiwuwar harin nukiliya ba, amma har da wasu illoli ciki har da karancin abinci. Hakan ba zai kasa nasaba da cewar, Ukraine da Rasha na cikin kasashen da ke fitar da muhimman abubuwa kamar Alkama da takin zamani da man girki. A Jamus alal misali, yanzu man girki ya zama tamkar lu'u lu'u, saboda daga Ukraine ake shigo da man girki, sanfurin Sunflower. Sai dai tarayyar Turai ta ce bata fuskantar barazanar karancin abinci, saboda nahiyar na iya ciyar da kanta daga abinda take nomawa, sabanin Afrika da ke dogaro da sayen Alkama daga Rasha da Ukraine. Sai dai ko a Turan yanzu manoma na fama da matsaloli na rashin abincin ciyar da dabbobi irinsu masara. Sai dai matakin fadar gwamnati na Kremlin na haramta fitar da alkama da takin zamani da masarar, ya fara yin nakasu a wurare da dama.
Kamun ludayin 'yar siyasar Afirka kuma shugabar Tanzaniya mace ta farko, Samia Suluhu.
Abubuwa da dama sun sauya a yayin da wasu nan nan inda suke cikin shekara daya na mulkinta" da haka ne jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bude labarin da ta buga a kan kamun ludayin 'yar siyasar Afirka kuma shugabar Tanzaniya mace ta farko, Samia Suluhu. Jaridar ta ci gaba da cewa, bayan mutuwar magabacinta John Magufuli, mai shekaru 62 da haihuwar Samia Suluhu Hassan ta ja hankalin kafofin yada labarai da manufofinta. Da farko dai ta kaddamar da shirin allurar rigakafin corona kana ta karfafa hulda da da dangantaka da kasashe makwabta, ba wai a Afirka kadai ba, hatta a wasu nahiyoyi ta cimma sake jan hankalin masu zuba jari zuwa Tantaniya.Yunkurin baya bayannan na inganta zamantakewa shi ne, ganawar shugaban kasar da manyan 'yan adawan kasar biyu. Daya da ya bar kasar bayan harbin bindiga sau 16 a shekarata 2017 da kuma na biyun da aka sake daga kurkuku. Hakan ya sa mutane yakinin cewar, shugaba Samia na da burin mayar da kasar tafarkin demokradiyya, kuma hakan abun yabawa ne. Sai dai duk da haka, ana ganin da sauran rina a kaba, musamman ma duba da cewa ita 'yar siyasa ce mai sanyin ba kamar marigayi Magufuli da ke daga murya, kuma duk da haka yana da masoya ciki da wajen kasar.