1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'asar kisan kiyashi a Ruwanda shekaru 17 da suka wuce

April 7, 2011

MƊD ta ware ranar bakwai ga watan afrilu domin kasancewa ranar ƙasa-da-ƙasa don tunawa da ta'asar kisan kisahin da aka fuskanta a Ruwanda kimanin shekaru 17 da suka wuce.

Ta'asar kisan kiyashi a Ruwanda a shekara ta 1994Hoto: AP

A daidai ranar bakwai ga watan afrilun shekara ta 1994 ne dai 'yan Hutu dake da rinjaye a ƙasar suka gabatar da matakinsu na kisan ƙare dangi akan 'yan Tutsi da kuma wasu 'yan Hutu dake da sassaucin ra'ayi. To sai dai kuma tun daga wannan lokaci al'amura sun canza suka ɗauki wani sabon fasali a ƙasar dake ƙunryar tsakiyar Afirka.

An samu ci gaba a fafutukar ɗinke ɓaraka

Alal-haƙiƙa dai babban abin da shugaban ƙasar Ruwandan Paul Kagame ya sa gaba shi ne tabbatar da aƙidar sulhu da ƙaunar juna tsakanin 'yan ƙasar, wadda ya ce ta zama abar koyi tsakanin ƙasashen Afirka. An saurara daga bakin Florent Janvier, babban sakataren gamayyar waɗanda tasa'asar ta rutsa da su a birnin Kigali, yana mai faɗin cewar:

Kotun sulhu a RuwandaHoto: Simone Schlindwein

"An cimma nagartaccen sakamako mai ba da ƙwarin guiwa bisa manufa. Gwamnati tayi bakin ƙoƙarinta wajen ɗinke ɓarakar dake akwai inda aka wayi gari ba wani banbanci tsakanin 'yan Tutsi da 'yan Hutu. Dukkansu al'uma ce ɗaya ta ƙasar Ruwanda."

A zahiri dai ba wanda ke batu game da Tutsi da Hutu sai dai 'yan ƙasar Ruwanda kawai. Sai dai kuma duk da haka akwai ƙwararrun masana dake taka tsantsan game da matakan sasantawar. Misali wata da ake kira Julia Viebach dake cibiyar binciken al'amuran sulhu ta jami'ar Marburg, ko da yake ta yaba da namijin ƙoƙarin da gwamnatin Paul Kagame take yi, amma kuma ta ƙara da cewar:

"Matsalar dake akwai ita ce kasancewar matakin gwamnatin a hukumance ta mayar da 'yan Hutu tamkar masu laifi, sassan su kuma 'yan Tutsi tamkar waɗanda aka yi wa laifi. Irin wannan rarrabewar tana hana ruwa gudu wajen cimma ainihin manufar da ake buƙata ta kyakkyawan zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da juna tsakanin sassan biyu."

An samu 'yan Hutu da suka ba 'yan Tutsi kariya

Abin nufi a nan kuwa shi ne, ko da yake akasarin waɗanda suka tafka ɗanyyen aikin 'yan Hutu ne, amma kuma an samu wasu daga cikin 'yan Hutun da ta'asar ta rutsa dasu sakamakon kariyar da swuka ba wa 'yan Tutsi. Shugaba Paul Kagame dai yana yaba wa ƙasarsa sakamakon ci gaban da take samu, wadda kuma ya ce tana iya zama abar koyi ga sauran ƙasashen Afirka. A ɓangaren tattalin arziƙi da zamantakewa dai ko shakka babu Ruwanda ta samu ci gaba kuma tana iya zama abar misali a nahiyar Afirka. Amma duk da waɗannan nasarorin ana sukan lamirin manufofin shugaba Kagame a cewar Julia Viebach:

Ruwanda na samun bunƙasar tattalin arziƙiHoto: James Nzibavuga

"Abin dake akwai shi ne ƙayyade 'yancin 'yan jarida da ikon faɗin albarkacin baki da gwamnati ke yi. Ƙungiyoyin farar hular dake akwai, dukkansu masu biyayya ne ga gwamnati a saboda haka suka samu ikon ci gaba da wanzuwa. Hakan ma ta fito fili a zaɓe na baya da aka gudanar, inda Kagame ya lashe kashi 90% na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa. Dukkan yunƙurin da 'yan hamayya suka yi gabanin zaɓen ya ci tura kuma akan irin wannan sibga ba za a samu wani ci gaba na demokraɗiyya ba a ƙasar."

A cikin watan fabarairun da ya wuce ne dai kotun ƙoli ta Ruwanda ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan kurkuku akan wani shugaban 'yan hamayya bisa zarginsa da laifin barazana ga makomar tsaron ƙasar. Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-Adam ta Human Rights Watch ta kwatanta wannan hukunci tamkar mummunan koma baya ga 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma manufofin demokraɗiyya a ƙasar. Wato dai a taƙaice Ruwanda tana da sauran tafiya gabanta kafin ta wayi gari tamkar abar koyi a nahiyar Afirka.

Mawallafi: Elisa Cannuel/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal