1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'aziyyar tsohon Firaministan Isra'ila

January 12, 2014

Shugabannin ƙasashen duniya sun fara miƙa sakon ta'aziyyarsu ga al'ummar ƙasar Isra'ila bisa mutuwar tsohon Firaministan kasar

Hoto: Reuters

A sakonsa na ta'aziyya shugaban Amirka Barack Obama ya ce za a riƙa tuna Sharon ɗin da sadaukar da rayuwarsa da ya yi wajen samar da ƙasar Isra'ila. Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yaba masa bisa tattaunawar da ya yi da kuma umartar sojojin Isra'ila da su janye daga yankunan Zirin Gaza na Palasɗinun. Za dai a fara gudanar da jana'izarsa a gobe Litinin, inda za a girmamashi. Ariel Sharon ya mutu ne yana da shekaru 85 a duniya bayan da ya kwashe shekaru takwas yana cikin halin rai kwa-kwai, mutu kwa- kwai inda yake numfashi da taimakon na'ura.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane