1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba ka Lashe 06.12.2017

Yusuf Bala Nayaya
December 7, 2017

Yayin da marubutan adabi suka sa himma a kokarinsu na rubutu da ma lika littafai da makalolinsu a shafukan intanet satar fasaha na yi musu kafar ungulu.

Marubata na Hausa na kokari a wannan zamani wajen ganin ba a barsu a baya ba, inda suke fafutikar ganin sun yi gogayya da takwarorinsu na sauran harsuna wajen yada harshen Hausa a shafukan intanet don mabiya a fadin duniya.