Taba Ka Lashe: 07.11.2018
November 9, 2018Talla
A farkon watan Nuwamban al’ummar Sayawa a kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro da ke a jihar Bauchin Najeriya suka gudanar da bikin raya al’adunsu na gargajiya da suka saba yi a kowace shekara. Kamar yadda suka saba a bana ma sun gudanar da shagulgulan bikin wanda ake wa take da Lim Zar.