Taba Ka Lashe: 09.08.2017
August 10, 2017Talla
Wani rukuni na masu matsakaicin karfi na karuwa a sassa dabam-dabam na kasashe masu tasowa, wanda ke kawo canje-canje masu tarin yawa kan yadda mutane ke amfani da lokacinsu na hutu, inda da yawa ke zaban zuwa kasashen ketare don yin hutu na shekara.
A dangane da haka su ma Musulmi 'yan yawon buden ido sun fi sha'awar zuwa wurare da ke da tanade-tanade irin na addininsu, musamman a Turai da ake wa lakabi da Halal Holidays.