Taba Ka Lashe: 10.05.2017
May 11, 2017Talla
Tuni dai aka kai wasu daga cikin 'yan gudun hijirar a wasu otel-otel a biranen kasar ta Girika suna jiran yanke hukunci game da bukatar neman mafaka da suka shigar. Birnin Thessaloniki da ke zama na biyu mafi girma a kasar ta Girika, na daga cikin biranen da aka tsugunar da bakin 'yan gudun hijira, kuma daukacin mazauna birni sun yi maraba da sabbin makwabatan na su.