Taba Ka Lashe: 10.12.2014
December 11, 2014Talla
Sakamakon sauyin zamani a wannan lokaci, al'adar auren Hausawa a kasar Chadi na fuskantar barazana ko ma bacewa baki daya, saboda shigar da wasu al'adu da aka ara daga 'yan kasar, abin da wasu ke cewa wannan wani babban koma baya ne ga kyawawan al'adun Hausawa, yayin da wasu ke da ra'ayin cewa idan zamani ya dinka riga sai ka dauka ka saka.