Taba Ka Lashe: 11.10.2017
October 12, 2017Talla
Harkar Almajirci na ci gaba da jawo hankulan kungiyoyi da daidaikun mutane kan tarin matsalolin da almajirai ke fuskanta wadanda an kasa warware da dama daga cikinsu. Da kudurin inganta harkar almajircin ne wata kungiya a Najeriya ta shirya taron ‘yan jarida don neman gudunmowarsu wajen wayar da kan al’umma.