1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 12.08.2015

August 14, 2015

Jami'ar Bayero da ke Kano a arewacin Najeriya ta shirya taron shekara-shekara na nazarin wakokin Zamani ko nanaye.

A tarayyar Najeriya manyan shehunan malaman harshen Hausa ne suka baje kolin iliminsu a nazarin wakokin Hausa a yayin taron "ga fili ga mai doki" na bana da sashen nazarin harsunan Nijeriya a Jami'ar Bayeru ta Kano ke shiryawa a ko wace shekara, inda ake gayyato mawaka su baje kolin su su kuma manazarta su yi nazarin wakokin tare kuma da fede su.