Taba Ka Lashe: 13.06.2018
June 15, 2018Talla
A wannan makon za mu duba wani batu ne na tarihi musamman ma da wani rikici na yanki da ya rikide zuwa wani yaki mafi muni a tarihin duniya. Yakin da ake wa lakabi da yakin shekaru 30 aka fara ne shekaru 400 da suka wuce a matsayin yakin addini amma ya sauya zuwa gwagwarmayar neman iko a Turai. Yakin ya bar mummunan tabo a Jamus. Wata yarjejeniyar zaman lafiya ta tarihi ta kawo karshen yakin. Wasu 'yan siyasa da masana tarihi sun yi imanin cewa yarjejeniyar zaman lafiyar ka iya ginshikin warware rikice-rikice na zamanin nan da muke