Taba Ka Lashe: 15.07.2015
July 16, 2015Talla
Tun shekaru aru-aru ake girmama 'yan bori a kasar Hausa a matsayin likitoci, wadanda ke yi wa mutane jinya ta han ya amfani da iskoki. Sai dai bayyanar rukiya ta sa sannu a hankali tasirin 'yan bori ya dakushe har ma ake musu kallon wadanda aikinsun ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.