Taba Ka Lashe: 17.+18.02.2016
February 19, 2016Talla
A wani matakin farfado da al'adun gargajiya da ke neman dushewa biyo bayan watsi da al'umma ta yi da su, a jamhuriyar Nijar wasu magadan gargajiya ne irin su sarakuna ke yunkurin maido da martabar al'adun domin nuna wa matasa irin muhimmancinsu ga rayuwar yau da kullum. A kan haka ne a kwanakin baya a yankin Bambey na jihar Tahoua aka gudanar da wasannin gargajiya da ake wa lakabi Sarho.