Taba Ka Lashe (22.03.17)
March 23, 2017Talla
Kambari yare ne da ke cikin manyan kabilu guda uku na a yankin Rijau. Yongo gari ne da ke birnin Amina, karkarar da a 'yan watannin baya bayannan ya dauki hankalin jama'a lokacin da aka fara yayata hotunansu a shafukan sada zumunta. Batu da ya fi daukar hankali dai shi ne yadda suturarsu ta ke musamman mata wadanda basa rufe wani bangare na jikinsu.