Taba Ka Lashe: 23.11.2016
November 24, 2016Talla
A kwanakin baya ne a birnin Kwalan na nan Jamus aka yi bikin fina-finan Afirka inda aka gabatar da jerin fina-finai daga nahiyar. Daya daga cikinsu shi ne wani fim mai taken "The Rising of the Son" wato "Da ya yunkuro" wanda wani mawaki dan kasar Saliyo ya shirya tare da hadin guiwar wasu matasa da suka taba yin irin rayuwar gararamba kan titi a Saliyo.