Taba Ka Lashe: 28.03.2018
March 29, 2018Talla
A kwanakin baya ne shugaba Emmuel Macron na Faransa ya kaddamar da wani shiri mai cike da babban buri da nufin mayar da harshen Faransanci daya daga cikin manyan harsuna na duniya musamman ma a nahiyar Afirka da ke zama gida ga mafi akasarin masu amfani da harshen na Faransanci.
Sai dai yayin da wasu masu kishin harshen Faransanci ke yaba wa shirin da aka ware kudi na miliyoyin Euro don bunkasa harshen Faransanci, masu sukar lamiri musamman 'yan Afirka sun ce shirin na da wata manufa ta sabon salo na mulkin mallaka.