Taba Ka Lashe: 28.06.2017
June 30, 2017Talla
Kungiyoyin 'yan hayan gida a kasar Spaniya sun nuna rashin jin dadinsu da wani abinda suka kira rikicin haya da ke tilasta 'yan haya barin gidajensu. Kungiyoyin na fatan kai kukansu ga gwamnatin kasar don ankarar da ita cewa samun gidan haya a manyan biranen kasar irinsu Barcelona da Madrid na kara yin wahala, musamman ga karamin karfi, saboda tashin gwauron zabi da kudin hayan ke yi.