Taba Ka Lashe: 29.11.2017
December 5, 2017Talla
Tatsuniya na daga cikin al'adar Bahaushe na kaka da kakanni wanda ya kunshi ba da labari na al'adun gargajiya da habaici da karin magana da raha. A takaice dai ya kunshi zamantakewa ta rayuwar al'umma. Tatsuniya ba koyar da ita ake yi a makaranta a matsayin darasi ba, sai dai iyaye da kakanni na labarta shi ga 'ya'ya ko jikoki a matsayin wani ilmi na fatar baka.