Taba Ka Lashe: (30.+31.12.2015)
January 3, 2016Talla
Hukumar masu fassara da tafinta ta Najeriya ta yaba da gudunmawar da kafofin yada labarai ke bayarwa wajen fassara sakonnin da ake bukatar su isar ga al'umma. Hukumar ta yi wannan yabo ne a lokacin babban taronta da masu ruwa da tsaki a harkar fassara da tafinta daga bangarori daban-daban suka halarta wanda kuma a karon farko Jami'ar Bayero da ke Kano ta dauki bakoncinsa.