Taba Ka Lashe: Zamantakewar al'umma a Filato
February 15, 2022
Talla
Al'adar zamantakewar jama'a a wasu biranen Filato ta sha bam-bam, inda Musulmi ke zama a unguwa dabam, Kiristoci suna zama a unguwanin Kirista wuri dabam. A shekarun baya dai ana zama a wuri guda ana cudanya a wuri daya, to amma yanzu lamarin ya sauya. Sakamakon yada al'amuran tsaro suka samu koma baya. Jihar Filato dai na daya daga cikin Jihohin Najeriya masu yawan ma'abiya Addinin Kirista, inda a karo da dama ake samun tashe-tashen hankula tsakanin Musulmi da Kirista.