Kalubalen sana'ar wanzanci a Afirka
January 22, 2019Talla
Wanzamai mutane ne da suke gudanar da sana'a da aka sani a kasar Hausa, inda suke kan gaba wajen yi wa yara kaciya musamman maza da aski da wasu abubuwan da suka danganci lafiya, amma mutane galibi sun koma asibitoci sannan aski da ya rage a hannun wanzaman, sannan za a iya cewa masu aski na zamani sun yi kakak gida a bangaren askin. Shugaban wanzamai da ke binrin Yamai na Jamhurriyar Nijar, Moussa Wansaba ya ce har yanzu ana samun yaran da suke yi wa kaciya, kuma a irin wannan lokaci na hunturi galibi ake yin kaciyar, sai dai ya ce daya daga cikin matsalolin da ake gani idan sun yi kaciya ga yara maza shi ne katsalandan da wasu ke yi wa sana'ar. Ku biyo mu a cikin shirin.