Taba Ka Lashe: Tsarin masarautar Damagaram
October 30, 2018Talla
Mai martaba sarkin Damagaran Sultan Aboubacar Oumarou Sanda a cikin tattaunawar da aka yi shi a cikin shirin Taba Ka Lashe ya tabbatar da cewar masarautar wace ta samo tushe tun kafin zuwan 'yan mulkin mallaka, na da al'adunta wadanda aka dade ana yin aiki da su.
Sai dai kuma ya ce da yake zamani ya sauya don haka dole suka sauya tsari don yin daidai da zamanin domin jin dadin al'umma. Mai martaba Sultan Aboubacar Oumarou Sanda ya ce babban sakon da ke gareshi a wajen al'umma shi na tabbar da samar da zaman lafiya da kuma girmama al'adu na yankin.