Taba Ka Lashe(11-01-2018)
January 12, 2018Talla
A tsawon shekaru 54 da yayi yana waka Jonny Halliday ya walla fayafayi ko album 81 na wakoki da ya yi rikodin su a kasashe daban daban na Turai da Amirka a cikin harsunan Faransanci da Italiyanci da Spaniyanci da ingilishi kana a cikin salon kida na Rock' n Roll da Bluse da dai sauransu.
Salon saka tufafin da na askin Jonny Halliday ya zamo abin yayi ga matasan kasashen Afirka musamman rainon Faransa kamar irin su Nijar kasar da ya ziyarta tare da gabatar da wakoki a watan Mayun 1968.