1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tababa game da ingancin salon siyasar Masar

May 17, 2013

Duk da iƙirarin da jamiyyar 'yan uwa musulmi ke yi na wanzar da demokraɗiyya a ƙasar Masar, 'yan adawa na zargin cewa tsarin da ta ke bi ya gocewa tafarkin demokraɗiyya

Bildnummer: 59152402 Datum: 30.01.2013 Copyright: imago/Sven Simon Präsident Mohammed MURSI Pressegespräch beim Staatsbesuch des ägyptischen Präsidenten im Bundeskanzleramt in Berlin, Deutschland am 30.01.2013. People Politik x0x xsk 2013 quer Aufmacher premiumd aktuellPolitik 59152402 Date 30 01 2013 Copyright Imago Sven Simon President Mohammed Mursi Press interview the State Visit the Egyptian President in Federal Chancellery in Berlin Germany at 30 01 2013 Celebrities politics x0x xSK 2013 horizontal Highlight premiumd aktuellPolitik
Mohammed MursiHoto: Imago

A Masar a yanzu haka, babu ƙungiyar da ta fi tasiri a siyasar ƙasar kamar ƙungiyar 'yan uwa Musulmi wato Muslim Brotherhood. Ita dai ƙungiyar ta kwatanta kanta a matsayin ƙungiyar da ke bin tafarkin demokraɗiyya, to sai dai rahotannin da ke fitowa daga ƙasar na nuna akasin hakan, abunda kuma ke sanya alamar tambaya kan sahihancin tsarin na hukumomin na Alƙahira.

Osama Dorra ya kasance mamba a ƙungiyar ta 'yan uwa musulmi na tsawon shekaru 10 kafin ya juya musu baya a shekarar 2011. Tun lokacin da ya ke makarantar sharar fagen shiga Jami'a wani daga cikin abokan sa ya ba shi labarin ƙungiyar wadda aka haramta, wadda kuma ta ke gudanar da ayyukanta cikin sirri a wancan lokacin.

Jamiyyar 'yan uwa musulmi na ba da mahimmanci ga ɗa'a

Yayin da ƙasar ke ƙarƙashin mulkin kama karyan tsohon shugaban ƙasa Hosni Mubarak ko ɗaya babu wahalar samun mambobi domin ana musu kallon waɗanda ke kwatanta adalci da kuma waɗanda ke yin addinin Islama na gaskiya to sai dai ba da daɗewa ba ya fara samun matsala da tsarin shugabancin da suke amfani da shi:

"Abun ya yi nisa har ya kai ga wasu suna sumbatan hannuwan manyan 'yan ƙungiyar, shi ya sa ni ko an bani aikin yi ban cika bada gaskiya wajen ba. Ko ɗaya basu cika so mutun ya bi yin kansa ba, sai dai ya daraja doka"

Osama DorraHoto: DW/M. Sailer

Wannan dalili ne ma ya sa Osama bai shiga ƙungiyar cikin hanzari ba, a cewar Osama duk wanda ya nuna yana da ɗa'a da biyayya zai sami ɗaukaka cikin hanzari, a kuma ƙara mi shi albashi. Albashin dai na da mahimmanci saboda kowani mamba ya kan baiwa ƙungiya kashi 7 cikin 100 na albashin na sa.

Yasser Mehrez mai magana da yawun kungiyar ya bayyana mahimmancin da ɗa'a ke da shi ga ƙungiyar kuma ya ƙaryata zargin makauniyar biyayyar da ake musu:

"Haka ne masu adawa da mu suke bayyanamu ga kafofin yaɗa labarai da ƙasashen waje, amma wannan ba haka bane, muna da 'yancin walwala wajen tunani da aiki, kuma ƙungiyarmu na ƙunshe da mutane masu basiri sai dai muna matuƙar ba da mahimmanci ga ɗa'a"

Yasser Mehrez ya cigaba ya kwatanta ƙungiyar a matsayin wadda ke wanzar da demokraɗiyya domin a ƙungiyar a kan ɗauki shawara daga mafi ƙanƙanta har zuwa mafi girma, haka nan kuma a majalisar ƙolin kungiyar wadda ake kira Shura akan zaɓi mambobin ne kamar yadda tsarin demokradiyya ya tanadar.

Matsala a yanayin rabon iko tsakanin 'yan ƙungiya

Mutane 19n da ke kwamitin zaɓen ƙungiyar ke zaɓen waɗanda zasu kasance a Schuran. Amma duk da haka ga Osama Dorra ƙungiyar ba ta wani bin tafarkin demokraɗiyya:

"Ko ɗaya abunda su ke yi ba demokraɗiyya ba ce, duk wani babba a ƙungiyar na da ɗalibansa, waɗanda ke masa biyayya, kuma idan za'a yi zaɓe, kuma waɗannan mutane da ke dogaro da mallaminsu sukan yana goyon bayan wani, su ma zasu mara masa baya"

Haka nan kuma ƙwararru na tababan sahihancin kwamitin ƙolin, Ba da daɗewa ba Khalil Anani daga jami'ar Durham ya soki tsarin cewa kwamitin zaɓe ya sanya ido kan majalisar ta Schura domin a ra'ayinsa kamata ya yi a ce ita Schura tana sa ido kan kwamitin zaɓe.

Yasser MehrezHoto: DW/H. Bdewi

A gare sa, tunanin cewa dole kowa ya kasance da ra'ayi na biyayya da kuma fargabar rasa iko su suke kwatanta masa yanayin siyasar ƙungiyar, wato shugabancinsu a yanzu yana mai da hankali ne wajen kare iko. Shi ya sa wasu ke kwatanta yadda mabiya ƙungiyar ke yawan ƙalubalanta masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Mursi tun watan Disemban 2012 a wannan tafarki.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman