Tabarbarewar tsaro a Najeriya na ci gaba da daukar hankali
May 16, 2014A sharhin da ta rubuta mai taken, man fetir, cin hanci da rashawa da kuma ayyukan tarzoma, jaridar Handelsblatt cewa Najeriya kasa ce mai arziki amma a lokaci daya kuma tana fama da talauci da tashe-tashen hankula da ka iya durkusar da kasa. A cikin farin ciki da annashuwa a kwanakin baya hukumomin kasar sun sanar cewa yanzu Najeriya ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka karfin tattalin arziki bisa sabbin alkalumman da ke nuni da jimillar kayakin da kasar ke samarwa a cikin gidan, to sai dai mene ne amfani wannan karfin arziki ga fiye da mutane miliyan 100 a kasar da ke rayuwa cikin matsanancin talauci? Ina kuma amfaninsa inda hukumomi suka gaza samar wa talakawa muhimman ababan more rayuwa, ga rashin tsaro sakamakon tashe-tashen hankula da suka addabi sassa daban-daban na kasar? Duk da makudan kudaden da ake ware wa fannin tsaro har yanzu kasar ta kasa shawo kan wannan matsalar. Saboda haka wasu masana ke zargin cewa wasu daga cikin manyan hafsoshin sojin kasar da gwamnoni da 'yan kasuwa suna arzuta kansu da kansu da kudaden da aka ware wa aikin yaki da ta'addanci.
Batun tsaro ya mamaye taron tattalin arziki
Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel kwatanta kungiyar Boko Haram ta Najeriya ta yi da kungiyar Taliban ta Afirka. Ta ce a gun taron tattalin arzkin duniya a kan Afirka da ya gudana a Abuja a makon da ya gabata, an mayar da hankali kan batun tsaro maimakon na tattalin arziki. Hakan ya faru ne saboda tashe-tashen hankulan da Najeriya ke fuskanta wanda kuma kungiyar ta Boko Haram ke da hannu ciki. Abin mamaki ga mutane da yawa shi ne yadda kungiyar ta shafe watanni tana aikata ta'asa ba tare da gwamnati ta dauki kwararan matakan kawo karshen su ba. Wani abin mamaki ma shi ne yadda kungiyar ta mallaki makaman yaki na zamani ciki har da motoci masu sulke.
Kotun duniya ga Sudan ta Kudu
Idan muka leka kasar Sudan ta Kudu kuwa har wayau jaridar Der Tagesspiegel ce ta yi tsokaci a kan halin da ake ciki a kasar tana mai cewa mayaka na zargin juna da aikata laifin kisan kare dangi a yakin basasan kasar ta Sudan ta Kudu. Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da kafa wata kotun hukunta laifukan yaki ga Sudan ta Kudu. A ranar Juma'a ta makon da ya gabata shugaba Salva Kiir da madugun 'yan tawaye kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar suka amince da shirin tsagaita wuta a matsayin ginshikin ci gaba da tattauna batun wanzar da zaman lafiya. To sai dai tun ba a kai ko ina ba bangarorin biyu sun fara karya ka'idojin yarjejeniyar.
Mutuwar 'yar jaridar Faransa a Afirka ta Tsakiya
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung labarin ta buga game da mutuwar Camille Lepage wata 'yar jarida mai daukar hoto da ke shiga wuraren da ba mai son zuwa. A cikin irin wuraren nan ne kuwa Camille Lepage mai shekaru 26 'yar kasar Faransa ta gamu da ajalinta. Wasu sojojin Faransa suka tsinci gawarta tare da na wasu mutane hudu a wani wurin binciken ababan hawa da ke yammacin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a bayan wata akori kura ta sojojin sa kan Kiristoci na wannan kasa.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu