1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da allurar riga-kafin Corona a Afirka

Mohammad Nasiru Awal ZMA
May 18, 2021

A ranar Litinin Afirka ta Kudu ta fara zagaye na biyu na allurar riga-kafin Corona ga wadanda shekarunsu suka haura 60. Hakan na zuwa ne yayin da kasashen Afirka ke samun jinkiri wajen yin riga-kafin.

Beitbridge Grenzübergang zwischen Südafrika und Simbabwe
Hoto: Guillem Sartorio/AFP/Getty Images

A yayin da ake samun sabbin nau'o'in kwayar cutar Corona da ke zama babbar matsala a fadin duniya, a Afirka har yanzu ana fuskantar jinkiri na yi wa al'umma allurar riga-kafin Corona. Yanzu haka dai kasashe da dama a nahiyar ba su sami kashi na biyu na riga-kafin ko dai saboda rashin niyya ko kuma rashin kudi. Kwayar cutar kuma na iya samun isasshen lokacin yaduwa.

Wai shin me ya sa yekuwar allurar riga-kafin ke tafiyar hawainiya ne? Me kuma ya kamata a yi domin gaggauta abubuwa? Morena Makhoana shi ne shugaban kamfanin harhada magunguna na Biovac da ke kasar Afirka ta Kudu, kamfanin kuma da ake dora kyakkyawan fata kansa na samar da allurar riga-kafi ga nahiyar Afirka. A hira da DW ya yi bayani yana mai cewa.

Karin bayani: Corona ta cika shekara daya a duniya

"A ganina batu ne na tsare-tsare shi ya sa ake samun tafiyar hawainiya. Za ka iya yi wa mutane riga-kafi ne idan kana da magunguna a hannu. Gaskiya abin na da nasaba da sauri ko jinkiri na samar da magungunan. Amma ina gani kawo yanzu an yi rawar gani."

Sai dai a lokaci daya ana korafi na rashin samun isassun alluran ga nahiyar Afirka, kuma a wasu kasashen kamar Malawi an zubar da alluran riga-kafin saboda rashin yarda da kuma rashin iya gudanarwa. Afirka ta Kudu, ko da yake ta yi odar isassun alluran ga kashi 75 cikin 100 na al'ummarta amma yanzu haka abin da ya isa kasar bai taka kara ya karya ba.

Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

A daidai lokacin da kasashe masu arziki ke mahawara kan yi wa yara riga-kafi, galiban mutane 'yan kasa da shekaru 60 aAfirka ta Kudu ba su san ranar da riga-kafin zai kai kansu ba.

Duk da matukar bukatar samun riga-kafin har yanzu ba a samar da shi a Afirka, ko me yasa ne? Morena Makhoana na kamfanin harhada magunguna na Biovac ya yi karin haske.

Karin bayani: Coronavirus: Zirga-zirga a iyakokin Afirka

"Ana bukatar abubuwa da dama wajen samar da riga-kafi. Yana kuma tattare da kasada. Kawo yanzu Afirka ba ta da karfin samar da muhimman sinadaran da ake bukata. Dole ne ka fara tun daga tushe idan kana son ka taka rawar a zo a gani. Kana kuma bukatar kwarewa da kayan aiki na zamani."

Burin Kungiyar AUshi ne ta yi wa kashi 60 cikin 100 na al'ummar nahiyar allurar riga-kafin Corona kafin karshen shekarar 2022. Sai dai ga yadda abubuwa ke tafiya yanzu zai yi wahala ta cimma wannan burin.