Fafatawar Falasdinawa da sojan Isra'ila
May 15, 2019Wannan rikici na zuwa a yayin gangami na tunawa da ranar Nakba da suke kira ranar "tashin hankali" kamar yadda Falasdinawa ke bayyana ranar ta tuni da lokacin da aka kirkiri kasar ta Isra'ila a shekarar 1948. Suna tunawa da wannan rana ne dai a irin wannan lokaci duk watan Mayu inda suke gangami na zanga-zanga da a lokuta da dama ke rikidewa zuwa tashin hankali.
Jami'an lafiya a bangaren na Falasdinawa sun ce wasu mutane sun samu raunika a har gitsin yayin da wani da ya sheda lamarin ya ce ya ga yadda sojan na Isra'ila ke amfani da ruwan kwata suna fesa wa Falasdinawan da harba masu hayaki me sa hawaye da ma amfani da harsashin roba. Mai magana da yawun sojan na Isra'ila ta bayyana cewa akwai kimanin masu zanga-zanga 1200 wadanda ke tunkarar iyaka da Isra'ila soja na amfani da dabaru na tarwatsa zanga-zanga suna korarsu.