1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimaka wa Somaliya da maƙudan kuɗaɗe

February 24, 2012

Babban taron ƙasa da ƙasa kan makomar Somaliya a London ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar ta magance matsalolinta.

The President of Somalia, Sheikh Sharif Ahmed (C) speaks, as the President of Kenya, Mwai Kibaki (L) and Prime Minister of Somalia TFG, Abdiweli Mohamed Ali, listen during the London Conference on Somalia at Lancaster House in London February 23, 2012. Britain's Prime Minister David Cameron said on Thursday that a failure to end Somalia's chaos will endanger international security, and the time is right for the outside world to help the failed state get back on its feet. REUTERS/Matt Dunham/pool (BRITAIN - Tags: POLITICS CRIME LAW CONFLICT)
Hoto: REUTERS

A wannan makon dai jaridun na Jamus gaba ki ɗaya sun mayar da hankali ne kan babban taron ƙasashen duniya game da makomar Somaliya da aka gudanar ranar Alhamis a birnin London na ƙasar Birtaniya.

Taimako ga tarayyar Somaliya yadda jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung ta fara rahotonta kenan game da taron, tana mai cewa:

"Bisa ga dukkan alamu firaministan Birtaniya David Cameron ya gano Somaliya, domin ƙasarsa ta zama wata ƙasar nahiyar Turai ta farko da ta sake naɗa wani jakada ga ƙasar, amma saboda dalilan tsaro a Mogadishu, daga birnin Nairobin Kenya jakadan zai riƙa gudanar da aikinsa. Firaministan ya kuma yi kira da a matsa ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyar al-Shabab da ya ce babbar barazana ce ga duniya, sannan a ranar Alhamis ya karɓi baƙoncin taron duniya na tara kuɗaɗen taimako ga Somaliya da gwamnatin wucin gadin ƙasar sai kuma tsananta yaƙi da 'yan fashin teku."

Taron kyakkyawan fata ga Somaliya inji jaridar Neues Deutschland tana mai nuni da taron na birnin London.

"Bisa bayanan firaministan Birtaniya David Cameron taron wani mataki ne na kyautata makomar Somaliya bayan shekaru kimanin 21 tana fama da rigingimu. Lokaci na ƙara ƙurewa domin yanzu a Somaliya kusan kowane lungu na ƙasar ya zama filin daga, inda kusan a kullum ake sace yara ana tilasta musu shiga aikin soja. Yayin da har yanzu wasu sassan ƙasar ke fama da masifar yunwa. Sannan ƙasar ba ta da wata sahihiyar gwamnati dake aiki. Saboda haka taron na London ya zama wani gagarumin mataki na neman hanyar magance rikicin ƙasar bayan tsaikon da aka samu na tsawon lokaci."

Dogon turanci na kawo ciƙas ga zuba jari

Daga rikicin siyasa sai na tattalin arziki. A rahoton da ta rubuta mai taken tattalin arzikin Afirka Ta Kudu yayi rauni, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa:

Hoto: picture-alliance/ZB

"Ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka ba ta ɗaukar hankalin kamfanoni masu zuba jari saboda yawan dogon turanci da rashin kyakkyawan yanayin zuba jari ga kamfanoni idan aka kwatanta ta da sauran ƙasashen duniya da tattalin arzikinsu ke haɓaka a wannan lokaci. A cikin watanni uku hukumar ƙimanta darajar ƙasa ta Fitch and Moddy's ta rage ƙarfin tattalin arzikin Afirka Ta Kudu bisa la'akari da raunin tattalin arzikin ƙasashen dake tafiyar da hulɗar cinikaiya da ita."

Dagwalon kayakin lantarki-barazana ga lafiya

Daga batun raunin tattalin arziki sai na bunƙasar harkar dagwalon nau'rar lantarki dake ci-gaba da yaɗuwa a nahiyar Afirka duk da matakai da kuma dokokin ƙasa da ƙasa da suka yi hani ga zubar da irin waɗannan shara ba bisa ƙa'ida ba. A tsokacin da ta yi akan wannan batu jaridar Tageszeitung cewa ta yi:

"Yankin yammacin Afirka na ƙara zama wani jujin tsoffin kayakin lantarki da suka lalace kamar akwatunan telebijin, komfutoci da wayoyin salula saboda ƙaruwar buƙatar waɗannan kayakin a ƙasashen yankin musamman janhuriyar Benin, Cote d'Ivoire, Ghana, Laberiya da kuma Najeriya. Rashin tsabtattun hanyoyin sarrafa tsoffin kayan, wasu na ƙona wayoyin domin samun tagulla. Wannan na haddasa gurɓatar yanayi da shaƙan hayaƙi mai guba. Kasancewa ɗaukacin wannan sharar lantarkin daga nahiyar Turai suke fitowa, ya zama wajibi gwamnatocin waɗannan ƙasashen su kafa dokoki masu tsauri na hukunta masu harkar tura tsaffin kayan lantarki zuwa Afirka.

Hoto: picture-alliance/ dpa

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu