1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Kaduna: Taimakon makarantun almajirai

November 14, 2024

Wata babbar Mujami'a a kudancin jihar Kaduna da ke Najeriya, ta rarraba kayan karatu a makarantun almajirai da nufin karfafa ilminsu da kuma zamantakewa tsakanin Kiristoci da Musulmi.

Najeriya | Almajirai | Karatu
Akwai tsangayoyin karatun almajirai da dama da ake fatan hada musu da karatun boko Hoto: DW

Kiristocin wannan Mujami'a karkashin jagorancin Pastor Yohanna YD Buru dai, na fatan ganin yara almajirai sun zurfafa ilminsu na addini da da na zamani kamar sauran yaran da ke zuwa neman ilmi a fadin duniya. Pastor Buru ya jagoranci tawagar mabiyansa zuwa wata tsangaya, ya bayyana cewa  sun sayo Alluna da Tawada da Alkalami domin rarrabawa wadannan yara almajirai, domin suma suna da hakkin da ya wajaba akansu wajen tallafa wa ilmin wadannan yara.