1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lai Ching-te ya samu nasara a zaben Taiwan

Abdourahamane Hassane
January 13, 2024

Dan takarar zaben shugaban kasar Taiwan da China ta bayyana a matsayin babban hatsari saboda matsayinsa na neman 'yanci,shi ne ke kan gaba da yawan kuriu a wani bangare na sakamakon zaben da aka bayyana a hukumance.

Lai Ching-te jagoran Taiwan
Lai Ching-te jagoran TaiwanHoto: Ng Han Guan/AP/dpa/picture alliance

Mataimakin shugaban kasa mai barin gado Lai Ching-te, na jam'iyyar Democratic Progressive Party (DPP), ya samu kashi 41.6% na kuri'un da akada a  kashi 60% na rumfunan zabe da aka kirga. Babban abokin hamayyarsa Hou Yu-ih, mai shekaru 66, dan takarar jamiyyar KMT dake kusantar China, ya samu kashi 33.2%.Yayin da  dan takara na uku, Ko Wen-je, mai shekaru 64, daga karamar jam'iyyar Taiwan People's Party (TPP) , ya zo na uku da kashi 25.3%.