1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ce-ce ku-ce kan ziyarar Tinubu cikin wani sabon jirgi

August 19, 2024

Kasa da kwanaki goma da kammala wata zanga-zangar neman gyaran lamura shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu na kan hanyar zuwa birnin Paris cikin wani sabon jirgin da ke jawo takkadama cikin kasar a halin yanzu.

Hoto: imago/STAR-MEDIA

 Can cikin watan Aprilun da ya shude dai, sai da ta kai ga shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu komawa zuwa ga jirgi na haya a kokari na ziyara a kasar Saudi Arabiya. To sai dai kuma shugaban ya jawo kace-nace cikin kasar sakamakon wani sabon jirgin da ya iso kasar kuma ke shirin dauka ta shugaban zuwa wata ziyarar a cikin birnin Paris .

Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Dalar Amurka miliyan 150 ne dai aka ce an saye jirgin ko bayan wasu dala miliyan 50 da aka kashe wajen sauya masa fasali ya dace da bukata ta masu mulki na kasar. A wani abun da 'yan kasar ke yi wa kallon wadaka a cikin yanayin babu.  Sanata Umar Tsauri dai na zaman wani jigo a cikin jam‘iyyar PDP ta adawa: ''Tun lokacin da Tinubu ya hau mulki kowa ya san waye shi, mutum ne da ba ya sauraron kowa, ba ya ganin daraja kowa. Ko majalisar kasa ba ta san da sayen jirgin ba. Ka ga wannan ya nuna maka, Tinubu na abun da ya ga dama ne. Wannan ya rage ga  'yan Najeriya.‘‘Siyasa cikin batun jin dadi, ko kuma wadaka cikin ruwa na talauci dai, sabon jirgin na zuwa ne kasa da tsawon makonni guda biyu da kammala wata zanga-zangar neman sauya rayuwa da makoma cikin kasar. An dai yi asara ta rayuka da daman gaske, ko bayan dukiyar da ta bata.

Hoto: DW/Z. Umar

To sai dai kuma   sabon jirgin a fadar Abdul Aziz Abdul Aziz da ke zaman kakaki na gwamnatin ta Abuja na zaman na wajibi ga tarayyar Najeriya a halin yanzu.‘‘ Jirgi ne da wani Balarabe dan kasuwa ya yi amfani da shi kafin daga baya wani a kasar Jamus ya karbe shi, kuma aka yi gwanjonsa, Najeriya ta saya. Kuma garabasa aka samu saboda da sabo za a saya sai an ninka kudinsa sau kusan uku. Kuma sayen jirgin ya zama dole, saboda shugaban kasa ya kai wata ziyara wata kasa, sai neman wani jirgin aka yi , saboda wannan ya samu matsala. Sabon jirgin dai na zaman daya a cikin jirage guda ukun da wani kamfanin kasar China ya kwace kafin daga baya ya sake shi  zuwa tarayyar Najeriyar domin amfani na  shugaban kasar.