Takaddama akan Sundukan makamai tsakanin Najeriya da Iran
April 30, 2013Wani alkalin kotun tarayya da ke birnin Legas a Najeriya, ya jinkirta yanke hukunci game da shari'ar da ta shafi wani jami'in rundunar juyin juya halin kasar Iran da ake zargi da hannu wajen safarar makamai ba bisa ka'ida ba ta Najeriya. Azim Aghajani - dan asalin kasar ta Iran, da kuma Ali Abbas Jega- dan Najeriyar da ake zarginsa da hadin baki da shi wajen safarar makamai ta tashar jiragen ruwan Najeriya dai, sun bayyana a gaban kotun - a wannan Talatar, yayin da alkalin kotun tarayya Okechukwu Okeke ya bayyana cewar saboda sarkakiyar da ke tattare da shari'ar ta su, yana bukatar karin lokaci domin yanke hukunci a ranar 13 ga watan Mayun nan da ke tafe.
Shi kuwa Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Chris Uche, cewa yayi yana da kyakkyawar fatan cewar hukuncin kotun zai wanke Azim Aghajani, dan Iran din daga zargin da ake yi masa.
Dama dai a shekara ta 2010 ne hukumomi a Najeriya suka tsare wasu manyan Sundukai ko kuma Kontenoni 13 dauke da makamai a tashar jiragen ruwn Apapa da ke Legas a Najeriya, inda suka yi zargin cewar dan kasar ta Iran na kokarin safarar su ne zuwa kasar Gambia, kuma tun cikin watan Fabrairun 2011 ne ake yiwa dan Iran din shari'a tare da wani dan Najeriyar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou