Takaddama game da kafa gwamnatin hadin kan kasa a Nijar
August 2, 2013Wanann lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da ya rage 'yan awoyi kalilan shugaban kasar ta Nijar ya gabatar da jawabinsa ga 'yan kasa albarkacin zagayowar cikon shekaru 53 da samun 'yancin kan kasar inda zai yi bayani kan batun karkare wanann shiri nasa.
To sai dai bisa dukkan alamu assalatu na kan hanyar warwarewa koma ta warware inji Malam Sabo Seidu mataimakin shugaban jam'iyyar MDC YARDA mamba a kawancen jam'iyyun adawar na ARN biyo bayan wani taro da shugabannin jam'iyyun adawar suka shirya a ranar Juma'a a birnin Yamai domin nazarin sakamakon da wata ganawa da shugabannin 'yan adawar suka yi da shugaban kasa a ranar Alhamis kan batun.
Takaddama kan mukamin firaminista
A ranar Alhamis dai shugaban kasar Nijar ya yi wata ganawa ta musamman da
shugabannin 'yan adawar a fadarsa da nufin karkare zancan shigarsu cikin gwanmnatin hadin kan kasar da zai tabbatar a cikin jawabin da zai gabatar wa 'yan Nijar cikin jawabin nasa na ranar Juma'a to amma taron nasu ya watse baram-baram bayan da shugaban kasar ya sanar da su cewa zancan ba su mukamin firaminista bai taso ba, kamar dai yadda shugaban jam'iyyar PNDS TARAYYA na riko Malam Bazum Muhamed ya yi ma gidan rediyon DW karin bayani.
Sai dai ga bisa dukkan alamu akwai baraka a cikin jam'iyyar MNSD NASARA madugar 'yan adawa a kan wanann batu domin kuwa wasu daga cikin kusoshin wannan jam'iyya da ba su so in nadi muryarsu ba sun ce ya zuwa yanzu jam'iyyar tasu ba ta kai ga tsaida magana daya ba a kan batun a yayin da kuma wasu daga cikinsu suka ce labudda matsayin da kawancen 'yan adawar na ARN ya dauka shi ne matsayin jam'iyyar ta MNSD NASARA. Ko ma dai mai ake ciki a ranar Asabar ake yinta ta kare wai 'yan magana suka ce ramamme ya zagi maye inda kawancen jam'iyyun adawar na ARN zai fitar da sanarwa inda zai bayyana hakikanin matsayin nasa dangane da wanann batu na shiga gwamnatin hadin kan 'yan kasa biyo bayan jawabin da shugaban kasar.
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal