Rikicin siyasa kan cire babban alkalin Najeriya
January 28, 2019Rikicin dai na kara cakudewa ya zuwa ranar yau kuma bangarori na kasar na dada jan daga, a cikin rikicin dakatar da babban alkalin Najeriya da gwamnatin kasar ta yi a makon da ya shude.
Can kuma a hedikwatar lauyoyi na kasar dai kungiyar lauyoyin tana shiri da ta taru da nufin sanin mataki na gaba a cikin neman mafitar rikicin da ke zaman mai tasiri ga kasar. Kokarin bin doka ko kuma gaban kai dai shi kansa shugaban kasar ya ce matakin dakatar da babban alkalin na bisa umarnin kotun da'ar ma'aikatan kasar da ke da alhakin gurfanar da Walter Onoghen da kuma ta nemi shugaban kasar ya dakatar da shi.
Shi kansa Onoghen din dai yaki kiran babban taron majalisar hukunta alkalai ta kasar da nufin nazarin zargin kin baiyana kaddarorinsa, abun kuma daga duk alamu ya harzuka 'yan mulkin Najeriya wajen kai wa ga hukuncin da ake yi wa kallon ya saba wa doka.
A gobe talata ne dai aka tsara majalisa za ta gudanar da zama da nufin nazarin mafitar rikicin da ke neman yin tasiri har a cikin kotun koli.