1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan yaki da rashawa a Najeriya

April 15, 2022

Yan Najeriya na dasa ayar tambaya kan afuwar da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi wa wasu tsoffin gwamnonin da ke zaman gidan kaso bisa laifin cin hanci da rashawa.

Nigeria Wahlgesetz
Hoto: Nigeria Prasidential Villa

A wani abun da ke iya janyo gagarumin koma baya a cikin yakin cin hanci a Najeriya, gwamnatin kasar ta yi afuwa ga wasu tsoffin gwamnoni guda biyu da ke gidan yari da aka samu da laifin satar dubban miliyoyin nairori. Jolly Nyame da ke zaman tsohon gwamnan jihar Taraba da kuma Joshua Chibui Dariye da ya mulki jihar Filato, na zaman manyan 'yan siyasa da ke gidan yari a yanzu a cikin yakin cin hancin Najeriya.

Sama da naira miliyan dubu daya da dari daya, kotun kolin tarrayar Najeriyar ta tabbatar tsohon gwamnan na Taraba Dariye ya sace daga aljihun gwamnatin Filaton a yayin kuma da Nyame ya sace miliyan dubu daya da dari shida. An yankewa Dariye hukunci na shekaru goma a gidan yari a yayin kuma da Nyame zai yi zaman kaso na shekaru goma sha hudu.

To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba dai gwamnatin kasar ta ce tai afuwa ga tsoffin gwamnonin guda biyu. Shugaba Muhammadu Buhari kuma a fadar Ministan shari'ar tarrayar Najeriyar Abubakar Malami, ya amince da sakin tsoffin 'yan jam'iyyar mai mulki ko bayan wasu 'yan kasar 157 da suka hada da tsofifn manyan hafsoshin soja.

“ Tsarin mulki na kasa musamman sashe na 175 karamin kaso na daya ya ba shugaban kasa dama na yin aiyuka na jinkai bisa wadanda aka yanke wa hukunci, musamman wadanda aka yankewa hukuncin zaman kaso, ku kisa ko makamancin wannan, ta la'akari da wannan dama shugaban kasa ya kafa kwamitin jin kai da yin afuwa a karkashi na kwamitin kuma yayi aiki ya gabatar da mutum 162 a matsayin wadanda ya kamata shugaban kasa ya duba domin yin wannan jin kan watau gafartawa ko rage tsananin hukuncin”

Duk da cewar dai afuwar laifin na zaman al'ada a cikin tarrayar Najeriya, kuma masu siyasa na kasar sun sha amfana walau akan tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasar Salisu Buhari da Shugaba Obasanjon ya ce, ya yi wa afuwar, ya zuwa tsohon gwamnan jihar Bayelsa DSP Alameiyeseigha da Shugaba Goodluck Jonathan ya ce, ya wanke, sabon matakin ya janyo kace-nace cikin kasar a halin yanzu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani