Takaddamar sauya kudin Najeriya
February 9, 2023Ya zuwa yanzun dai akalla Triliyan biyu da miliyan dubu Dari Shida na kudin kasar na Naira ne babban banki na kasar ya yi nasarar janyewa a cikin shiri na komawa zamani cikin hada-hadar kudi a Najeriya. Adadin kuma da ya ninka har kusan gida tara na yawan sabbabin kudaden da bankin ya yi nasarar samarwa da nufin cike tsohon gibin.
Karin Bayani:Rudani kan kin karbar tsoffin takardun Naira
Duk da tsoma baki da kafa daga kotunan dai ya zuwa wannan Alhamis layuka suna kara tsawo a bankunan da ke fadin babu kudi. Ita kanta kwarya-kwaryar nasarar gwamnonin guda uku dai daga duk alamu ta gaza kai wa ya zuwa sauya tunani na jami'an babban bankin da suke ci gaba da rike sabbabi da su kansu tsofaffin kudin.
Duk da kiran neman sauki a tsakanin al'umma dai tana kara fitowa fili bukata ta kudi yayin zabe na zaman ta kan gaba a cikin ummul' aba'isin raba garin tsakanin gwamnatin kasar da abokan burminta na gwamnonin jam'iyyar APC. Akwai tsoron janye batun kudi a siyasar na iya kai wa ga ba za ta cikin sakamkon da ake shirin gani bayan zaben. To sai dai kuma a fadar Buba galadima da ke zaman jigo a cikin jam'iyyar NNPP ta adawa ana iya tantance bukatar talakawa da masu neman mulki da kudi.
Rikicin rashin tsaro da talaucin da ya mamaye kasar bayan annoba ta Korona, ko bayan sauyin kudin da ke ta jawo rikici cikin kasar a halin yanzu dai na shirin zama na kan gaba wajen yanke hukunci a bangaren 'yan kasar da ke neman hanyar inganta rayuwa a halin yanzu.