Takaddama tsakanin Rasha da Amirka kan rikicin Siriya
June 21, 2017Jirgi na biyun da Amirkar ta kakkabo a cikin mako guda a kasar ta Siriya jirgi ne mai sarrafa kansa kirar kasar Iran. Jami'an Amirka sun ce a yanzu suna dab da tabbatar da ko rundunar juyin juya hali ta kasar Iran ce ta sarrafashi, bayan da ta ayyana fara kai hare-haren ramuwar gayya kan kungiyar IS a cikin Siriya, wacce ta kai wasu hare-haren ta'addanci cikin kasar ta Iran makwanni biyun da suka gabata.
Rundunar Sojin Amirkar dai ta futo karara ta bayyana cewa duk wani harin da za a kai wa Kurdawan da take ba wa kariya tamkar hari ne kanta.
A nata gefen rundunar sojin Rasha wacce ta siffanta kakkabo jiragen na Siriya da neman tsokana, ita ma ta yi barazanar kakkabo duk wani jirgin kawancen da ya keta kudancin kogin Furat, bayan da ta ayyana dakatar da tuntubar junan da take da Amirkar a yakin da suke da kungiyar IS.
Kawancen yaki da IS na fuskantar barazana
Tuni dai kasar Ostareliya ta sanar da ficewa daga kawancen da Amirka ke jagoranta na yaki da IS biyo bayan gargadin na Rasha.
Gwamnatin Siriya wadda a sannu sannu dakarunta ke kwato wuraren da suka kubuce musu a baya, ta ce kakkabo jiragen nata biyu babbar shaida ce kan yadda Amirka ke bada kariya ga 'yan ta'adda.
Masharhanta na tabbatar da cewa, duk wani taho mu gaman da za a samu a Siriya tsakanin Amirka da Rasha ba zai haifarwa kasar ta Siriya da mai ido ba.