1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta gargadi Rasha kan Ukraine

EBU ZMA
January 19, 2022

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg sun bukaci Rasha da ta kawo karshen abin da suka kira da yin kutse a kan iyakarta da Ukraine.

Deutschland Scholz und Stoltenberg in Berlin
Daga hagu zuwa dama Jens Stoltenberg sakatare janar na NATO da Olaf Scholz shugaban gwamnatin JamusHoto: Hannibal Hanschke/REUTERS

Kiran nasu ya biyo bayan fargabar da suke da ita kan cewa Moscow na shirin mamaye kasar ta Ukraine, inda suka zargeta da jibge sojojinta kimanin dubu 100 a kan iyakarta da Kiev. Scholz ya nunar da cewa Jamus da NATO na bukatar Rasha ta rage adadin dakarunta da ke kan iyakokinta da Ukraine din, ko kuma ta fuskanci tsauraran matakai daga gare su. A wata ganawar da ta yi da takwaranta na na Rasha Sergei Lavrov a birinin Moscow, ministar kula da harkokin ketare ta Jamus Annalena Baerbock ta jaddada muhimmancin warware wannan rikici cikin fahimtar juna duba da irin kyakkyawar alaka da ke tsakanin kasashen biyu.

Jamus na kokarin ganin an warware rikicin tsakanin RashadaUkraine cikin sulhu

Annalena Baerbock sakatariyar harkokin waje ta JamusHoto: SNA/imago images

Ta ce "Ina so in jaddada muhimmancin dangantakar da ke tsakanin tarayyar Rasha ga sabuwar gwamnatin Jamus da ni karan-kaina. Babu wani abun da zai iya maye gurbin alakar da ke tsakanin Moscow da Berlin, kuma zan ci gaba da dorawa a kan wannan alakar. Ina fadan haka ne a madadin sabuwar gwamnati".A daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke ziyara a birnin Kiev fadar gwamnatin Ukraine din, gwamnatin Biden ta sanar bayar da karin dalar Amurka miliyan 200 a matsayin tallafin a fannin tsaro ga gwamnatin Kiev da ke cikin fargabar mamayen Rasha.

A cewar sakataren harkokin waje na Amurka Antony Blinken babu dalilin jibge adadin wadannan sojojin da Moscow ta yi 

Antony Blinken sakataran harkokin waje na AmirkaHoto: Alex Brandon/AFP/Getty Images

Yace:" Cikin watanni da suka gabata hankalinmu ya koma kan Ukraine saboda ci-gaba da jibge sojojinta da Rasha ke yi a kan iyakokin Ukraine, ba tare da an tsokane ta ko kuma wani sahihin dalili ba, sai dai kawai tana da karfin soji. Kuma muna sane da cewar akwai shirin kara yawan sojojin ba tare da wata sanarwa ba. Kuma hakkan ne ya bai wa shugaba Putin damar aiwatar da hakan a wurarren lokaci, na afkawa Ukraine da karfin soji". Ana dai sa ran Blinken zai gana da shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine da kuma takwaransa na harkokin kasashen waje na Ukraine Dmytro Kuleba a fadar gwamnatin na Kiev. Ma'aikatar harkokin wajen na Amurka ta nunar da cewa rmakasudun ziyarar ta Blinken shi ne jaddada goyon bayan Washinton ga Kiev. Bugu da kari rahotamnni na nuni da cewar sakataren harkokin wajen na Amurka zai zarce zuwa birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, domin ganawa da takwararsa ministar harkokin waje Annalena Baebock, kafin daga bisani a ranar Juma'a ya gana da ministan harkokin ketare na Rasha Sergei Lavrov bayan wata tattaunawa da suka yi a Talatar wannan mako ta wayar Tarho.